9 Maris 2022 - 16:01
Iran Ta Yi Nasarar Harba Wani Tauraren Dan Adam

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sunyi nasarar harba wani tauraron dan adam, kusan shekaru biyu bayan harba tauraron dan adam na farko na soja.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Hukumar IRGC ta yi nasarar sanya tauraren mai suna Nour-2, cikin nasara kamar yadda shafin PRESSTV ya rawiato.

An harba tauraron dan adam din wanda kirar gida ne da na’urar harba tauraren dan adam mai hawa uku, wanda aka yi wa lakabi da Qased.

Ana sa ran tauraron dan adam Nour-2 zai gudanar da ayyukan soji da na farar hula a Iran, da suka hada da bincike.

342/